Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Buhari ya kara harajin iskar gas a Nageriya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta aiwatar da karin haraji da kaso 7.5 na iskar gas da ake shigo da shi kamar yadda farashin sa ya tashi da  kashi 100 cikin watanni 8 a Nageriya.

Shugaban kamfanin na kasa Michael Umudu ya ce akwai dalilai uku da ke haddasa karin farashin kashida kaso 70 cikin 100, na iskar gas da ake anfani dashi a Najeriya, musamman wajen shigo da shi daga kasashen waje.

Michael Umudu ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai, har ma ya ce, Nageria na shigo da kusan kashi 70 cikin 100 domin samar da wadatacciyar iskar gas.

Bayanai sun bayyana cewa farashin iskar gas mai nauyin kilo 12.5 wanda ake siyarwa akan farashin naira 3,500 a watan disambar 2020, yanzu tashin gwauron zabi zuwa 6,800 a Abuja.

Michael ya kuma ce gwamnatin tarayya ta kara harajin kayayyaki na VAT makonni uku da suka gabata da 7.5 wanda shine ya yi sanadin hauhawar farashin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!