Kasuwanci
CBN ya shirya taron faɗakar da jama’a kan hada-hadar Kuɗi

Babban bankin Najeriya CBN, ya shawaci mutane musamman ma ƴan kasuwa da su rungumi taarin yin amfani da sabbin hanyiyin hadadar kudi domin kauce wa samun matasala
Mataimakiyar Shugaban sashen yaɗa labarai ta bankin Hajiya Hakama Sidi Ali, ce ta buƙaci hakan yayin taron faɗakar da al’umma da CBN ya gudanar yau Talata.
Ta ce, “Yanzu lokaci ne da ya kamata a ce dukkan mutane su tabbatar suna yin amfani da sabbin hanyoyin sauƙaƙa mu’amalar kuɗi sabo kauce wa yan damfara da kuma samun kwanciyar hankali wajen yin mu’amalar kuɗi.”
Haka kuma ta ƙara da cewa, ” akwai hanyoyi da dama da ake amfani da su wajen hada-hadar kudi da suka haɗa da amfani da na’urar POS da kuma manhajar haskawa a waya yayin biyan kudi.”
Wadannan hanyoyi suna bayar da kariya matuƙa da kuma kwanciyar hankali musamman a irin wannan lokaci da ɓata gari ke zambatar mutane.
Da ya ke jawabi ga manema labarai yayin taron, shugaban ƙungiyar masu hada-hadar Kuɗi ta wayar hannu da kuma na’urar POS Malam Salihu A. Umar, ya yaba wa babban bankin na CBN bisa tsare-tsaren ya na mai cewa suna taimakawa matuƙa wajen warware matsaloli da kuma sama wa dimbin mutane ayyukan yi.
Taron dai ya samu halartar dubban mutane da suka haɗar da ƴan kasuwa da ma’aikatan jami’o’i da ɗalibai da matasa ƴan hidimar ƙasa da wakilan kamfanoni da dama.
You must be logged in to post a comment Login