Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Chairman Mariri Market Cup: Layin Auwalu Ragabza ya lashe gasar

Published

on

A wasan karshe na gasar cin kofin Mariri Cola Nut Market, da ake kira da Chairman Cup, wasan da aka buga tsakanin kungiyar kwallon kafar Layin Auwalu Ragabza da FC Kwata.

Layin Auwalu Ragabza ya samu nasarar lashe kofin mai taken Chairman Cup.

Hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu a kan FC Kwata da ci 2-1 a wasan da suka buga jiya 29 ga watan Oktobar 2021.

Dan wasan Layin Auwalu Ragabza mai suna Auwalu sisin kwalo da Abbatiyo ne suka zurawa kungiyar kwallon da ta basu nasara a wasan.

Yayin da dan wasan FC Kwata Jibril ya zurawa kungiyar sa kwallo 1 a wasan.

Dan wasan Layin Auwalu Ragabza Auwal Muhammad da akekira Auwal Sina ne ya fi zura kwallo a gasar inda ya ci kwallo 6 wanda hakan yasa aka bashi kyautar takalmin kwallo.

Da yake jawabi bayan tashi daga wasan shugaban kwamatin shirya gasar kuma shugaban kasuwar ‘yan Goro dake Mariri, Alhaji Salisu Auwal da ake Kira da Salisu Dan Alaye ya ce sunji dadi da yadda matasan kasuwar da al’ummar karamar hukumar ta Kumbotso suka karbi gasar.

A cewar sa a duk shekara za su rinka shirya gasar tare da Kara kawatata.

Shi kuwa shugaban karamar hukumar ta Kumbotso Hon. Hassan Garba Kauye Farawa cewa yai an shiya gasar ne dama domin samar da hadin kai tsakanin al’ummar karamar hukumar ta Kumbotso.

Ya kuma godewa kwamatin shirya gasar kan yadda suka shirya gasar ta kuma kayatar da mutane.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!