Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Wayne Rooney ya zargi ‘yan wasan Manchester United da yiwa Ole Gunner Solskjear bita da kulli

Published

on

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Wayne Rooney ya zargi ‘yan wasan kungiyar da rashin samun nasarar ta.

Yace dole sai sun dage wajen samun nasarori ba kawai a dora laifin rashin nasara ga mai horar da kungiyar ba Ole Gunnar Solskjaer.

Wanda a yanzu haka ke shan matsin lamba sakamakon rashin kokari da kungiyar batayi a kakar wasannin da muke ciki.

Mai horar da kungiyar Derby County ya nuna rashin jin dadinsa a wasan da Man United ta sha kashi da ci 5-0 a hannun Liverpool a makon da ya gabata.

Tsohon dan wasan kasar Ingila da Man United ya ce dole ne ‘yan wasan United su kara kaimi da kuma jajircewa muddin suna son nasarar kungiyar ta cigaba da samuwa.

“‘Yan wasan kansu akwai alamar su tambayi kansu duba da yadda kungiyar ke samun rashin nasara, bawai ace kawai mai horar da kungiyar za’a dorawa laifi ba,” a cewar Rooney.

Rooney ya shafe shekaru 13 a Old Trafford, inda ya lashe gasanni da dama a kungiyar da kuma nasarar zura kwallaye 253 a tawagar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!