Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Chelsea ta cimma yarjejeniya da Rennes a kan mai tsaron raga

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta amince da kungiyar kwallon kafa ta kasar Faransa Rennes, domin daukan mai tsaron ragar kungiyar, Edourd Mendy.

Chelsea na zawarcin mai tsaron ragar dan kasar Senegal mai shekaru 28, Edourd Mendy.

Duka kungiyoyin biyu sun cimma matsaya a kan kudi Fam miliyan 71.

Chelsea na neman maye gurbin mai tsaron ragar ta, Kepa Arrizabalaga tun bayan da a ke samun sabani da mai tsaron ragar ta Kepa.

Watsi da ayyukan gwamnati: Gwamnoni na kawo koma bayan ci gaban da Chelsea na ganin cewa mai tsaron ragar ta Kepa na daya daga cikin wanda ya jawo kungiyar ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Liverpool a gasar Firimiyar kasar Ingila da su ka fafata a ranar Lahadi.

Arrizabalaga mai shekaru 25 sai dai Chelsea ta sauya shi da mai tsaron raga Willy Caballero mai shekaru 38 a wasan karshe na cin kofin kalubale da kungiyar ta fafata da Arsenal.

Mai horas da Chelsea Frank Lampard, ya tabbatar da cewa yanzu hala Caballero ne zai tsare ragar kungiyar a wasan da za su fafata da Barnsley a ranar Laraba na kofin Carabao.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!