Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Wasan Sada Zumunta : Super Eagles ta gayyaci sabbin ‘yan wasa

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasa, Gernot Rohr, ya gayyaci karin ‘yan wasan kasar nan shida da suke taka leda a kungiyoyin kwallon kafa daban-daban a fadin duniya, domin shiga tawagar ‘yan wasan da zasu fafata a wasannin sada zumunta da kasar Ivory Coast da Tunisia.

Za dai a fafata wasannin ne a kasar Austria a ranar tara da kuma goma sha uku ga watan Oktoba mai zuwa.

‘Yan wasan sun hadar da Chidera Ejuke dake wasa a CSKA Moscow da Frank Onyeka dake taka leda a FC Midtjyllad da Samson Tijjani da Zaidu Sanusi dake FC Porto da Matthew Yakubu dake a SKF Sered da kuma Cyril Dessers.

Dan wasan Manchester City Gundogan ya kamu da cutar

Ya kamata gwamnati tayi dokar gwada lafiyar ‘yan wasa – Dr. Ayodeji

Wannan shine karo na farko da Najeriya ta mika goron gayyata ga ‘yan wasan guda biyar a cikin su, yayin da ya zama karo na biyu ga Cyril Dessers.

Gernot Rohr ya ce zai ajiye mai tsaron gida Francis Uzoho wanda a baya-bayan nan ya warke, sakamakon rauni da ya ji a wasan sada zumunta da aka fafata da kasar Brazil a shekarar da ta gabata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!