Kiwon Lafiya
Chibok:Shugaba Buhari ya ce gwamnati baza ta gajiya ba wajen kwato ragowar yan matan ba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada tabbacin gwamanatin sa baza ta gajiya ba wajan kwato ragowar yan matan chibok dake tsare a hannun yan boko haram.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a shafin sa na twitter a ranar lahadi,a yayin bikin tunawa da ranar da aka sace ‘yan matan chibok a makaran tar yan mata dake garin na chibok bayan shekaru biyar a jihar Borno a watan afrilu 2019.
Shugaban kasar yace kimanin dari da bakwai ne suka dawo gida daga cikin wadanda aka sace ,kuma ya jaddada aniyar gwamnatin tarrayya wajan kokarin ta na ceto ragowar yan mata dake hannun yan boko haram har da ma Leah Shuaibu wace aka sace tare da ‘yan matan sakataren Dapchi a jihar Yobe tare da duk wani dan kasar nan dake hannun ‘yan tayar da kayar baya.
Shugaban kasar Ya kara da cewa yayi alkawarin ceto ragowar ‘yan matan domin sada su da iyalan su, yana mai yin alkawarin ganin dukkanin wadanda aka sace sun shaki iskar ‘yan cin kai
Muhammadu Buhari yace dubannin mutane daka garkuwa dasu,tuni jamien tsaro kasar nan suka ceto su a cikin shekaru hudu da su ka gabata,kuma baza su gajiya ba har sai an dawo da su wurin iyalan su
Kuma ya taya yan matan murnar samu yanci daga wajan yan taadda tare da ci gaban da suka samu a rayuwa su daban daban