Labarai
Ci gaban ƙasa: Shugabanni su samar da kariya ga dukiyar al’umma – Dakta Aliyu Dahiru
Cibiyar hada-hadar al’amuran banki a Jami’ar Bayero da ke Kano, ta ce sai shugabanni sun bada kariya ga dukiyar al’umma sannan za a samu ci gaba.
Dakta Aliyu Dahiru ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi da shi ta cikin shirin Duniyar mu a yau na Freedom Radio.
Ya ce, haƙƙin kowanne shugaba ne bada kariya ga dukiyar al’ummar da ya ke jagoranta.
“Gina ƙasa shi ne ƙawata ta da rayata yadda jama’a za su ji daɗin zamantakewa da gudanar da Al’amuran su”.
“Shugabannin da basu da manufa na kasancewa koma baya a dukkanin lamari da tsarin jagorancin da za su gudanar” a cewar Dakta Aliyu Dahiru.
Malamin ya ƙara da cewa babu ƙasar da za ta ginu yadda ya kamata idan babu ingantaccen shugaba.
Dakta Aliyu ya kuma ce sai an ɗauko komai daidai, ta hanyar da ta da ce kana shugaba ya kasance ya mayar da hankali akan bayar da ilimi ingantacce ga Al’ummarsa.
Bai kamata shugaba ya mayar da dukiyar ƙasa aljihunsa ba saboda yana ɗaya daga cikin abunda ke rusa ƙasa”.
You must be logged in to post a comment Login