Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jihohi sun yi amfani da kudadden tallafin cutar Corona da muka basu – Sani Aliyu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce jihohin kasar nan sun yi amfani da kudadden tallafin cutar corona da ta basu domin kawo karshen annobar a fadin kasar nan.

Babban jami’in lura da kwamitin kar ta kwana na  fadar shugaban kasa kan yaki da cutar Corona a kasar nan Dakta Sani Aliyu, ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Dakta Sani Aliyu ya ce gwamnatin tarayya ta raba kudaden yaki da cutar ga gwamnatocin jihohi 32, na kasar nan naira biliyan dai –dai.

Sani Aliyu, ya kara dacewa kudaden an bada su ne ga jihohin don cigaba da yaki da cutar musamman ma wajen gwaji da bincike tare da daukar matakan kariya.

A nasa jawabin, shugaban hukumar dakile yaduwar cuttutuka ta kasa NCDC, Dakta Chike Iheakweazu, ya ce hukumar zata gudanar da binciken kariya da duba lafiyar al’umma na gida –gida a jihohin Lagos, da Gombe da Nassarawa da Enugu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!