Labarai
Cibiyar jagoranci nagari ta ‘Dantiye ta nada jami’in bata shawara kan tsaro
Cibiyar jagoranci nagari da bunkasa aikin Jarida ta Dantiye wato Dantiye Centre of Good Leadership and Journalism, DCLJ, ta sanar da daukar tsohon mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda Joshak Habila, a matsayin babban jami’in tsaron ayyukan zabe da tabbatar da zaman lafiya na yankin bangarori.
Hakan na kunshe ne a cikin sanawar da aka rabawa manema labarai a yau, mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin amintattu na cibiyar ta DCLJ, Farfesa Munzali Jibrin.
Takardar sanarwar ta kara da cewa, nadin na Habila ya zo ne sakamakon aiki tukuru bisa hazaka da yayi a matsayin sa na kwararren dan sanda.
Farfesa Jibril ya ce “a tsawon shekaru 30 da ka kwashe kana aiki, tabbas mun yaba maka wajen kwarewar ka ta shirya tsaro, daftari da tsare-tsare musamman na yadda za a shawo tare da kaucewa matsalolin tsaro dana zabe a cikin gida da kasashen ketare na Afirka”.
Don haka cibiyar na farin cikin da shigar sa da gudummuwar da zai bayar a cikin cibiyar, a kokarin da take na hadin gwiwa a cikin kasa da kasashen ketare wajen aiki kafada da kafada da ‘yan jaridu ta hanyar shigar da al’umma wajen tabbatar da jagoranci na gari samar da dumokaradiyya da aiki bisa doka.
Habila na daga kan gaba -gaba a kasar nan da ake cire musu hula akan sha’anin da ya shafi tsaro na ayyukan zabe, wanda shi ne fagen da ya kware tare da yin karatun sa na Digirgir a jami’ar Kalaba (Calabar) a shekarar 2007.
A baya-bayan nan dai cibiyar ta DCLJ, ta sanar da daukar tsohon ministan tsare-tsare na kasa Dakta Shamsudden Usman, a matsayin mai bata shawara na musamman akan tsare-tsaren tattalin arziki da bunkasa shi na bangarori.
You must be logged in to post a comment Login