Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Cikakken bayanin yadda kotu ta ɗage ci gaba da shari’ar neman sake gurfanar da Abduljabbar

Published

on

Lauyan da yake jagorantar lauyoyin gwamnatin jihar Kano, Barista Surajo Sa’idu ya bayyana wa kotu cewar gwamnati ta rubuta takardun tuhuma tare da roƙon kotun ta janye takardar tuhumar da ƴan sanda suka gabatar.

Kotun ta waiwayi lauyoyin Abduljabbar ko suna da wani jawabi kafin karanta tuhumar.

Anan ne Barista Sale Bakaro ya ce lauyoyin da suka zo kotu domin gabatar da tuhuma ba lauyoyin gwamnati bane.

Don haka ya bukaci ganin takardar da aka sahale musu a matsayinsu na lauyoyi masu zaman kansu da a yanzu suka zo a matsayin lauyoyin gwamnati.

Sai Barista Surajo Sa’idu ya ce ai lauya bashi da hurumin ya tuhumi lauya kan batun tsayawa a gaban kotu kuma ya bayyana cewa su bari a karanta takardar tuhuma sai su yi suka akai.

Daga nan kuma Surajo Sa’idu ya ɗakko takardar da kwamishinan shari’a ya basu a matsayin an sahale musu su gurfanar da malamin ya miƙawa kotun.

Kotun ta miƙawa lauyoyin Abduljabbar takardun sahalewar sai dai lauya Sale Bakoro ya ce, suna da suka akan takardar domin dokar da aka dogara da ita aka basu takardar bata cikin dokar kundin tsarin mulkin ƙasa.

Ya kuma ƙara da cewa takardar tuhumar da suka sake kawowa itama ta saɓawa doka.

Dan haka da kwamishinan shari’a da waɗannan manyan lauyoyi sun gaza kawowa kotu wata doka wadda kotu za ta dogara da ita.

“Wannan takardun zargi kamar ma babu su ne domin waɗannan manyan lauyoyi sune suka sanya hannu akan takardun kuma basu da hurumin zuwa su wakilci gwamnati,” inji lauya Bakoro.

Bakaro ya kuma bayyana cewar, “A shari’ar musulunci ba a sauaya da’awa ko ayi ƙari ko ragi kamar yadda su lauyoyin gwamnati suka yi a yanzu”.

A ƙarshe barista Bakaro ya ce, yana roƙon wannan kotun da ta sallami wannan manyan lauyoyi saboda ba su da hurumin zuwa wannan kotun.

Lauyan gwamnati barista Surajo Sa’idu ya bayyana cewar a doka idan har an kawo tuhuma a gaban kotu dole ne a karanta tuhumar sannan duk wata suka ta biyo baya.

Dan haka ya buƙaci barista Sale Bakaro da ya janye duk wata sukar da yayi a gaban kotu.

Kotun ta waiwayi barista Sale Bakaro wanda yace yana nan akan bakansa domin tun ranar 16 ga watan Yuli ƴan sanda suka gurfanar da Abduljabbar tare da karanta masa takardar tuhuma inda ya musanta.

Mai Shari’a Sarki-Yola ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali, kafin ranar 2 ga Satumba don yanke hukunci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!