Labarai
Ciki da Gaskiya: Bana cikin Gwamnonin da EFCC ta sanyawa ido – Ganduje
Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi watsi da rahoton jaridar Sahara Reporters da ya ce, yana cikin Gwamnonin da EFCC ke bincika a yanzu haka.
EFCC dai ta sanar da cewa, ta gano wasu Gwamnonin ƙasar nan uku sun ɓoye kuɗaɗe malala gashin tinkiya a gidajensu, inda suke yunƙurin biyan ma’aikata albashi a hannu.
Hukumar ta ce tana sanya idanu kan Gwamnonin amma bata bayyana sunayensu ba.
Wannan na zuwa ne bayan da babban bankin ƙasa ya sanar da shirin sauya fasalin wasu daga kuɗaɗen ƙasar nan.
Sai dai jaridar Sahara Reporters ta bayyana Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle dana Ribas Nysome Wike a matsayin waɗanda EFCCn ke sanyawa idanu.
To amma a sanarwar da Kwamishinan yaɗa labaran Kano Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Lahadi ya musanta rahoton.
Ya ce, rahoton na jaridar Sahara ƙanzon kurege ne, da ba shi da tushe balantana makama.
Kuma an yi hakan ne domin a ɓata sunan Gwamna Ganduje.
Kwamishinan ya ce, Kano na cikin jihohin da ke kan gaba wajen biyan albashin ma’aikata a kan kari ba tare da gazawa ba.
Gwamna Ganduje ya nemi jaridar da ta janye wancan labarin, sannan ta nemi afuwarsa, idan ba haka ba kuma zai ɗauki matakin shari’a.
You must be logged in to post a comment Login