Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Ganduje da wasu Gwamnonin Arewa sun tafi Oyo

Published

on

Gwamnonin Arewa maso yamma sun kama hanya domin zuwa jihar Oyo kan rikicin ƙabilancin da ke faruwa a jihar.

Mai taimaka wa Gwamnan Kano kan yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai shi ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio.

Yakasai ya ce, tawagar ta haɗa da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle.

Da kuma Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da na Kebbi Alhaji Atiku Abubakar Bagudu.

Gwamnonin sun kama hanyar ne bayan da suka kammala taron ganawa da masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro a Arewa wanda suka yi a jihar Kaduna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!