Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Cikin watanni 2 mutane 450 ne suka kamu da cutar Corona – Buhari

Published

on

Gwamnatin Tarayya, ta ce cikin watanni biyu a kalla yan kasar dari hudu da biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar corona.

Shugaban Kwamtin kar-ta-kwana na yaki da cutar Boss Mustapha ne ya bayyana hakan rahoton da ya fitar jiya Litinin.

Ya ce, ma’aikatan kiwon lafiya saba’in da biyar ne suka kamu da cutar a makon da ya gabata, ciki kuwa har da rahoton da ke nuna cewa mutum bakwai sun kamu da nau’in cutar corona da aka gano ta a Burtaniya.

Boss Mustapha ya nuna damuwarsa kan yadda jihar Lagos ke zama a mataki na farko na masu yawan cutar, tare da sauran kananan hukumomi 22.

Ya kuma ce akwai yiwuwar dakatar da tashin jirage daga Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!