Labarai
Cin hanci da rashawa: Haƙƙin kowa ne ya yaƙi matsalar da kansa – Barista Balarabe
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Kano ta ce, haƙƙin kowa ne ya yaƙi matsalar cin hanci da rashawa a duk inda yake.
Shugaban hukumar Barista Mahmud Balarabe ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani tattaki da hukumar ta shirya a wani ɓangare na bikin ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta duniya.
Barista Mahmud ya ce, daƙile matsalar cin hanci da rashawa a ko’ina a faɗin duniya na samun nasara ne idan aka samu haɗin kan al’umma.
“A Kano Muna s nasarar yaƙi da matsalar cin hanci da rashawa, domin kuwa idan aka kwatanta da shekarar bara za a ga an samu rahuwar matsalar”.
Ya ce “Maƙasudin shirya irin wannan tattaki shi ne ƙara janyo hankalin al’umma kan sanin muhimmancin ranar da kuma kira a kan su zama jakadun yaƙi da cin hanci da rashawa a kowane mataki”.
Majalisar ɗinkin duniya ce ta ware duk ranar 9 ga watan Disambar kowacce shekara matsayin ranar yaƙi da cin hanci da rashawa da nufin nusashshe da al’umma illolin da cin hanci ke da shi.
You must be logged in to post a comment Login