Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abin da ya sanya muke neman Dambazau – Anti Kwarafshin

Published

on

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta bada umarnin a kamo mata shugaban hukumar kare hakkin masu sayen kaya ta jihar Janar Idris Bello Danbazau mai ritaya.

Shugaban hukumar Barista Mahmud Balarabe ne ya bada umarnin biyo bayan zargin Danbazau din da karbar cin hanci.

“Ni na tura ma’aikata da yan sanda don su gayyato mana shi, kasancewar an akwo mana korafi a kansa, musamman wani mutuum da yayi korafin cewa an kama masa madara kuma an bukaci ya biya kudi kafin a sakar masa kayansa, kuma ya bayar amma ba a dawo masa da kayan ba”.

“Mun tura masa takarda da farko bai amsa ba, inda y ace mana baya gari amma har zuwa yanzu bai taba amsa gayyatar mu ba, mu kuma doka ce ta kafa mu don haka za ta yi aiki a kan kowa”.

Barista Mahmud ya kuma ce, da zarar hukumar ta kammala tattara bayanai akan Dambazau din za ta bayyana mataki nag aba.

Da yake batu kan koken wasu al’umma a Kano kan batun filaye, gida je da gonaki Barista Mahmud Balarabe ya ce “Za mu bincika koken al’ummar karamar hukumar Kumbotso kan yadda aikin layin dogo ya janyo musu rasa mahallansu ba tare da an biyasu diyya mai kyau ba”

“Mun sani gwamnatin tarayya ce ta ke yin aikin, sai inda aka samu matsalar shi ne rashin tuntubar hukumomin mu da su ma’aikatan kamfanin da yake aiki yayi, wanda kuma mun zauna da su mun fara tattauanwa”.

Shugaban ya kuma ce, a ranar Litinin mai zuwa ne hukumar za ta kafa kwamitin da zai bibiyi matsalar domin magancewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!