Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Cin Zarafi: Wata mata ta ƙyatta wa ƴar kishiyar ta ashana a matancinta

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wata mata mai suna Aisha Abdullahi Giade sakamakon zarginta da cin zarafin ‘yar kishiyarta.

Mai magana da yawun rundunar SP Ahmed Muhammed Wakil ta cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, wadda ake zargin ta lakada dukan kawo wuka ga ‘yar kishirta mai suna Zahra Abdullahi mai shekaru takwas (8).

Haka zalika Aisha Abdullahi ta zane Zahra da wayar wutar lantarki sannan ta kyatta a shana a cikin matocinta.

Tun farko dai sakatariyar kungiyar da ke rajin yaki da cin zarafin mata ta jihar Bauchi Talatu Musa ce ta kamo matar mai suna Aisha Abdullahi mazauniyar unguwar Kofar Durmi zuwa ofishin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi.

‘‘Zahra ta yaga kayanta ne lokacin da ta ke bacci lamarin da ya fusata kishiyar babarta wato Aisha Abdullahi ta dauki wayar wuta ta zaneta sannan ta kona matancinta da ashana, lamarin da ya janyo ta samu munanan raunuka’’ A cewar Talatu Musa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!