Kiwon Lafiya
Cibiyar CITAD ta bukaci kungiyoyin dalabai da malamai da su hada hannu wajen ciyar da makarantun su gaba
Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato CITAD ta yi kira ga kungiyoyin dalabai da malamai da su hada hannu wuri guda wajen ciyar da makarantun su gaba musamman ta bangaren koyarwar zamani.
Daraktan cibiyar Yunusa Zakari Ya’u ne yayi kiran yayin taron wayar da kai da cibiyar ta shirya da hadin gwiwar Rosa Luxemburg Foundation da kuma kungiyoyin dalibai kan yadda suke fuskantar kalubale yayin gudanar da ayyukan su da yadda za su ciyar da makarantunsu gaba, daya guda na jami’ar Bayero dake nan Kano.
Daraktan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da kuma gwamnati kan su mayar da hankali wajan samarwa dalinbai guraren karatu da kuma kayan karatun na zamani dan samun ingantatcen ilimi
A nasa bangaren tsohon shugaban kungiyar daliban jami’ar Bayero Sanata Khalid Sunusi Kani ya bayyana cewar ayanzu san rai ya mamaye ayyukan kungiyoyin Dalibai, inda ya ce galibin masu shugabantar kungiyoyin dalibai na kasar nan ba ma dalibai ba ne.
taron ya sami halartar kungiyoyin dalibai da Malamai, yayin da aka tattauna kalubalen da suke fuskanta da hanyar gyara su.