Connect with us

Coronavirus

Coronavirus ta kama ‘yan kwamitin yaki da cutar a Kano

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa shugaban Kwamitin kar ta kwana na yaki da cutar Covid-19 na Jihar Kano Farfesa Abdulrazak Garba tare da wasu mambobin kwamitin guda 3 sun kamu da cutar Corona.

Kwamishinan lafiya na Jihar Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran ma’aikatar Hadiza Namadi ta fitar yau.

Ta cikin sanarwar kwamishinan ya shawarci jama’a da kaucewa cakuduwa da juna sannan kuma su zauna a gidajensu, kuma gwamnatin Jihar Kano tana ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar cutar.

Kafin zuwan wannan rahoto dai mutane 21 ne aka sanar daewa sun kamu da cutar tare da mutuwar mutum guda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!