Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda al’ummar Kano suka karbi dokar hana fita da gwamnati ta sanya

Published

on

Tun da misalin karfe goma na daren jiya ne dokar hana fita da gwamnatin Kano ta sanar a matsayin wani mataki na dakile yaduwar cutar corona ta fara aiki.

Wakilan Freedom sun rawaito cewa titunan birnin Kano a yau Juma’a, sun kasance a share babu jama’a sosai, sai dai a wasu bangaren matasa sun mai da titunan wuraren wasanni.

A ranar Talata da ta gabata ne Gwamnatin jihar Kano ta sanar da kafa dokar hana fita wanda ya fara aiki da nufin dakile yaduwar cutar corona a fadin jihar.

A yau juma’a dai ita ce wayewar gari ta farko da al’ummar Kano su ka yi da wannan doka, inda gari yayi shiru, tituna suka kasance kamar kufai babu hayaniya kamar yadda aka saba yau da kullum.

Sai dai duk da haka, a wasu sassa na birnin Kano ba a rasa fitowar jama’a nan da can, inda wasu za ka gansu zaune bakin tituna ko shaguna sun yi jugum sun zura wa sarautar Allah Ido.

Freedom Rediyo ta zanta da wasu matasa a birnin Kano wadanda ta iske su suna wasan kwallon kafa akan tituna, inda suka bayyana cewa ganin yadda titunan ba kowa ne ya sanyasu gudanar da wasannin da suke.

A gefe guda kuma likitoci na bada shawarwarin yin tazara wanda na daya daga cikin shawarwari na kariya daga cutar, sai dai garesu wadannan matasa zaman cikin gida ne ya ishesu saboda haka ya sanya suka yi fitan dango a bakin tituna suna cin abinci.

Haka zalika suma wadannan matasa da suka kasance a gidaje sun shaidawa freedom Rediyo halin da suka tsinci kansu a yau, na zaman guri daya wanda a cewar su basu saba da hakan ba.

A yayin ziyarar dai da wakilan namu suka gudanar sunga yadda motocin daukar marasa lafiya ke ta zarya, yayin da a bangare guda jami’an tsaro su ka kakkafa shingaye akan tituna duk da nufin dakile yaduwar cutar corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!