Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Har yanzu bamu tsayar da makin samun gurbin shiga jami’a ba -JAMB

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa Jamb, ta ce har yanzu bata kai ga tsayar da makin jarabawar da dalibi zai samu kafin ya a bashi gurbi a jami’a.

Hukumar ta kuma bukaci al’ummar Najeriya musamman dalibai da kada su yadda da duk wani bayani da zasu samu kan batun makin inde ba daga hukumar ya fito ba.

Hukumar ta ce kawo yanzu ba za’a fitar da adadin makin ba, har sai an zauna taron masu ruwa da tsaki, karkashin jagorancin Ministan Ilimi na tarayya Malam Adamu Adamu, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 15 da 16 a watan yuni mai zuwa.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar Dr. Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya yi watsi da duk wasu rahotanni da ke yawo cewa hukumar ta fitar da adadin makin da ake bukatar dalibi ya samu kafin samun gurbi a jami’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!