Labaran Kano
Covid-19: Al’ummar kasar nan su kwantar da hankalin su kan aikin Hajjin bana-Fakistan
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, ta bukaci alummar kasar nan dasu kwantar da hankali su bisa ga umarin da hukumomin kasar saudiyya suka bayar na dakatar da dukanin shirye-shiryen aikin hajjin bana sakomakon cutar covid 19 ake fama da ita a duniya.
Shugaban hukumar Abdullahi Saleh Fakistan ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi nan freedom radiyo, wanda ya mayar da hankali kan umarnin dakatar da shirye-shiryen aikin hajjin bana da kasar Saudiyya ta bayar.
Ya ce har yanzu hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano na ci gaba da gudanar da shirye-shiryen ta, kasancewar wannan umarni har yanzu bai je wa hukumar, a hukumance ba.
A nasa bangaran shugaban kamfanin shirya tafiye-tafiye na Hamsun, Alhaji Mustafah Hamisu ce akwai bukatar wadanda suka riga suka biya kudaden sun a Umara da su kara hakuri, kasancewa kamfanoni irin nasu na kokarin mayar musu da kudaden su, kasancewar babu batun tafiya a halin yanzu.
Bakin sun kuma shawarci al’ummar musulmai da su kasance masu bin dokokin masana harkokin kiwon lafiya da gwamnati, tare da gyara tsakanin suda mahaliccin su, don ganin an shawo kan wannan annoba da ta addabi duniya.
You must be logged in to post a comment Login