Coronavirus
COVID-19: An horas da direbobin Adaidaita sahu dabarun kariya a Kano
Wata kungiya mai zaman kanta mai rajin dorewar ci gaban al’umma da ayyukan gina Bil-adama wato Sustainable Dynamic Human Development Initiative, ta horas da masu tuka baburan adaidaita sahu dabarun kare kai daga kamuwa da annobar Corona tare da raba musu sinadarin tsaftace hannu kyauta.
Yayin gabatar da jawabin wayar da kan nasu ƙungiyar ta koyar da yadda ya kamata su rika tsaftace hannayensu lokaci bayan lokaci saboda yadda suke karbar kudade daga hannun fasinjoji.
A cewar daraktan tsare-tsare na kungiyar Dakta Umar Abdullahi, ya ce “an shirya bada shawarwari da tallafin ne la’akari da yadda direbobin ke mu’amala da mutane da yawa ba tare da ɗaukar kwararan matakan kariya ba”.
Ita kuwa shugabar kungiyar Hajiya Aisha Ahmad Dangi cewa ta yi “kasancewar annobar ta COVID-19 cuta ce mai saurin yaduwa a tsakanin al’umma ya sanya kungiyar ta hada sinadarin na tsaftace hannu da nufin raba shi kyauta ga mutane”.
Ko ta ya ya ‘yan adaidaita sahu za su kare kansu daga kamuwa da cutar ta hanyar abubuwan da aka koya musu a taron? Tambayar da shugaban kungiyar masu tuka baburan na jihar Kano TOAKAN, Alhaji Sani Sa’idu Dan koli, ya amsa da cewa, za su yi amfani da dabarun da suka saba na amfani da sabulu da ruwa wajen tsaftace hannu kamar yadda suka koyar da mambobin nasu tun a baya kana sun koya musu yadda kungiyar ta basu shwarwarin kariya.
Haka Kuma Shugaban ƙungiyar ta TOAKAN ya yaba wa kungiyar bisa yadda ta zabo kungiyarsu domin bata tallafi.
Yayin taron dai, shugabar kungiyar ta kuma ce nan ba da jimawa ba kungiyar za ta fara koyar da masu tuka baburan yadda za su rika hada sinadarin da kansu su kuma rika yin amfani da shi.
Masu gudanar da sana’ar ta tukin baburan adaidaita sahun na jihar Kano, tun a baya sun sha bayyana cewa tsadar da sinadarin ke da ita ce ta sanya basa iya saye domin amfani da shi.
Sai dai kasancewar wannan kungiya ta raba sinadarin kyauta ga masu baburan tare da wayar musu da kai bisa yadda za su dauki matakan kariya daga annobar ta COVID-19.
You must be logged in to post a comment Login