Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun hallaka ‘yan bindiga a Zamfara

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta ce dakarunta na Operation Hadarin Daji sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga da dama tare da lalata maboyarsu da ke dajin Kuyanbana a Jihar Zamfara.

Shugaban sashen yada labarai na rundunar Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan ta ciki nwata sanarwa da ya fitar, yana mai cewar sojojin sama ne suka yi luguden wuta cikin dajin bayan samun rahotanni na sirri, da ke tabbatar da cewa maboya ce ta wani shaharren ‘dan bindiga mai suna Dogo Gede da jama’arsa.

Bayan fara luguden wutar ne sai ‘yan bindigar suka fara tserewa daga dajin a kan babura wasu kuma a kafa, daga nan ne sojojin suka hallaka su.

Ta cikin sanarwar, babban hafsan sojin saman kasar nan Air Marshal Sadique Abubakar ya jinjinawa jami’an sojojin bisa wannan nasara da suka samu, inda ya bukace su da kada su saurarawa duk wasu ‘yan bindiga da suka addabi al’ummar kasar nan.

Karin labarai:

Sojoji sun hallaka ‘yan Boko Haram 17 a Borno

Zamfara:rundunar yan sanda ta musanta rahotannin kai hari ga shaidun Atiku Abubakar

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!