Connect with us

Coronavirus

Covid-19: Cibiyar gwajin Corona zata fara aiki a Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa tace cibiyar gwajin cutar corona zata fara aiki daga ranar litinin mai zuwa a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar kuma shugaban kwamatin karta-kwana na yaki da cutar corona a jihar Jigawan shine ya tabbatar da haka ga manema labarai.
Dakta Abba yace tuni kayan gwaje-gwajen suka iso jigawa an kuma fara sanya su a wani sabon sashe dake cikin babban asibitin Dutse wato Dutse (General Hospital).
A cikin makon daya gabata ne dai gwamnatin jihar jigawa taci alwashin gina tata cibiyar, sakamakon kalubalen da take fuskanta na gwajin cutar.
Wakilinmu Muhd Aminu Umar ya rawaito kwamishinan na cewa cibiyar zata cigaba da aiki koda bayan Corona ta wuce, ta hanyar ci gaba da gwajin cutuka masu ya duwa.

Karin labarai:

Za a samar da kotun tafi da gidanka kan Coronavirus a Jigawa

Covid-19: Gwamnan Jigawa ya amince a gabatar da sallar idi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!