Connect with us

Labarai

Covid-19: Ganduje ya karawa ma’aikata hutun sati 2

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta karawa ma’aikatan jihar hutun sati 2 a wani bangare na ci gaba da tsaurara matakan hana annobar Covid-19 shigowa jihar Kano.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano Abba Anwar ya aikowa Freedom Radiyo a yammacin yau litinin.

Sanarwar ta ce Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar rahoton kwamitin gwamnatin jihar Kano na tattara tallafin cutar Corona wanda shugaban kwamitin Farfesa Yahuza Bello ya mika masa a fadar gwamnatin jihar Kano.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin wa’adin hutun sati 2 na farko da gwamnatin ta bayar ya kare a yau litinin, inda sanarwar ta ce  karin hutun  zai fara daga gobe talata 7 ga watan Aprilu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!