Connect with us

Labaran Wasanni

Da Dumi-Dumi: Mahaifiyar Guardiola ta rasu sakamakon Covid-19

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dake kasar Ingila ta sanar da rasuwar mahaifiyar mai horas da ‘yan wasan kungiyar Pep Guardiola sakamakon Cutar Corona.

Dolors Sala Carrio, mai shekaru 82 ta mutu ne a birnin Barcelona dake kasar Spaniya.

Guardiola mai shekaru 49, a kwanakin baya ya dai bada tallafin gudunmawar Yuro miliyan daya kwatankwacin Fam dubu dari tara da ashirin domin a yaki cutar Covid-19.

Tuni dai wasu kungiyoyin kwallon kafa suka fara aikewa da Guardiola da Man City sakon ta’aziyya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!