Connect with us

Labarai

Covid-19: Mutane 2 sun warke a jihar Legas

Published

on

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da cewa an sallami wasu mutane 2 da suka warke daga cutar Corona a Jihar.

Yanzu haka adadin wadanda aka sallama ya tashi daga 33 zuwa 35.

Sanwo-Olu ya ce mutanen biyu da aka sallama mace da namiji ne, kuma an gwada an gano sun warke daga cutar.

LABARAI MASU ALAKA

Covid-19: Ganduje ya karawa ma’aikata hutun sati 2

Covid-19: Kungiyar Youths Helping Hands ta bada tallafi a Kiru

Covid-19: Abokan mataimakin shugaban kasa za su bayar da tallafin naira Miliyan 100

To sai dai duk da wannan ci gaba da Jihar Legas ta samu, har yanzu ita ce kan gaba a cikin yawan mutanen da suke dauke da wannan cuta a jihohin Najeriya, inda  yawan masu fama da cutar ya kai mutane 120 yayin da birnin tarayya Abuja ke da mutane 48.

Jihar Osun tana da mutane 20, Edo 11, Bauchi mutane 9, 6 kuma a Akwa Ibom 5 a Jihar Kaduna, Ogun ma 5, sai 4 a jihar Enugu, 2 a Ekiti.

Sauran su ne Rivers mai mutane 2, Kwara ma biyu, Benue na da 1 yayin da Ondo ma ke da mutum 1.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!