Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Ganduje zai sanya ‘yan Firamare cikin tsarin koyar da karatu daga gida

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta fadada koyar da ‘yan makaranta data fara ta kafafen yada labarai na Radiyo da Talabijin zuwa ga makarantun Firamare a zaman da suke a gida don kare yaduwar cutar Corona data shigo kasar nan.

Kwamishinan Ilimi na jihar Kano Alhaji Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru, ne ya bayyana hakan a tattaunawar sa da gidan Radiyo Freedom kan yadda aka fara gudanar da shirin na koyar da yara ‘yan makaranta daga gida.

Alhaji Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru, ya kuma ce, sun fara duba yiwuwar ci gaba da gudanar da darusan ta kafafen yada labaran bayan an samu saukin annobar ta Corona.

Makwanni uku Kenan da gwamnatin jihar Kano ta fara gabatar da shirin koyar da yara ‘yan makarantar Sakandire daga gida ta akwatinan talabijin da kafar Radiyo.

Hakan ya biyo bayan zaman da yaran kanyi a gidajen iyayen su sanadiyyar hutun makarantu da gwamnati ta bayar don rage cakuduwar jama’a, a wani bangare na yakar cutar Corona da gwamnatin keyi.

Gwamnatin jihar ta Kano ta ce ta dau wannan mataki ne sakamakon rufe makarantu biyo bayan ci gaba da yaduwar cutar corona.

A cewar ta za a gabatar da shirye-shiryen koyar da daliban makarantun ne daga gida a kafafen yada labarai na Radiyo da talabijin mallakin gwamnatin jiha.

Kan hakan ne ya sanya Freedom Radiyo ta jiyo ra’ayoyin wasu iyaye a nan jihar Kano game da yadda suke kallon shirin na koyar da yara daga gida da gwamnati ta fara a wannan lokaci da ake fama da cutar Corona.

Haka zalika Freedom Radiyo ta zanta da wasu daliban sakandare game da yadda suke sauraren shirin.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!