Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Ganduje ya kirkiri shirin koyar da dalibai daga gida

Published

on

Gwamnatin jihar kano ta ce zata fara koyar da dalibai  ta kafar Radio da  talabijin, sakamakon rufe makarantu da tayi a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar Corona.

Kwamishinan Ilimi na jihar kano Alhaji Muhammad Sanusi ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Alhaji Muhammad Sanusi ya ce koyar da yaran zai bada dama yaran su cigaba da karatunsu daga gida.

Ta cikin sanarwar ta bayyana cewa a dai dai lokacin daliban Kananan ajujuwan makarantar sakandire  ke shirye shiryen zana jarabawa, mai maimakon su zauna a gida kawai zasu amfani da damar wajen cigaba da karatun su.

Alhaji Muhammad Yace zasu mayar da hankali ne wajan koyawa daliban darusan Ingilishi da kuma Lissafi da kuma sauran da rusa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!