Connect with us

Sharhi

COVID-19: Har yanzu ana samun haramtattun tashoshin mota a Kano

Published

on

Duk da dakatar da daukan fasinjoji, daga Kano zuwa wasu jihohin kasar nan da gwamnatin jihar Kano ta yi a wani yunkuri da take na yaki da cutar Covid-19 data bulla a wasu sassan jihonin kasar nan.

Wanda hakan yasa gwamnatin ta dauki matakin hana shige da fice a tsakanin iyakokin kano indai ba motar daukan abinci ce ba data dakon man fetur dana daukan kayan aiki na kamfanonin dake jihar nan.

Sai dai duk da irin wannan yunkuri da gwamnati tai na dakile tafiye-tafiye zuwa wasu jihohin kasar nan sai ga wasu direbobin motocin haya dake aiki zuwa jihohin kasar nan da aka dakatar da aikin nasu zuwa wani lokaci sabo da cutar ta Corona na ci gaba da gudanar da sana’ar tasu ta zuwa wasu jihohin kasarnan.

Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya leka wannan haramtarciyar tashar dake dorawar na Abbah gaban tashar Mariri inda direbobi ke gudanar da lodin Maiduguri da Jigawa da Bauchi da kuma Yobe inda suke daukan mutane zuwa wadannan garuruwa.

A wani bincike da wakilin namu ya gudanar a wanna haramtacciyar tasha ya gano cewa ana daukan fasinjan Jigawa kona Bauchi akan naira dubu biyu a dah yayin da yanzu suka kara kudin mota.

Kan haka ne wakilin namu Abubakat Tijjani Rabi’u ya tuntubi shugaban hukumar Karota Baffa Babba Dan’agundi ta wayar tarho kan ko hukumar tasan da wannan haramtacciyar tasha sai ya ce sun samu labari kuma yanzu ma haka tuni hukumar ta baza jami’anta don tabbatar da abinda ake zargin

Baffa Babba ya kuma ce duk direban motar da aka kama ya ketare iyakar Kano ko ya shigo da fasinjoji hukumar ta Karota zata gurfanar dashi a gaban kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Addini

Muhimman abubuwan da ya kamata ku sa ni kan Sheikh Ja’afar Mahmud

Published

on

An haifi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 ko da yake wani lokacin Yakan ce 1964.

Marigayi Sheikh Ja’afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a hannun Mijin Yayarsa, Mallam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini.

Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen Malam Umaru a wani gari  Koza, Kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai

dangantaka ta jini.

Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda  asalin sa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.

Kafin zuwan sa Kano, marigayi Sheikh Ja’afar ya riga ya fara haddar Alkur’ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.

Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur’ani mai girma, kasancewar sa mai sha’awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980,  ya shiga makarantar koyon Larabci  ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada Al ‘ Adun Misra.

Sheikh jafar ya kuma shiga makarantar Larabci ta  Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988.

A shekara ta 1989, ya sami gurbin karatu a jami’ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta Ilimin Tafsiri wanda kuma ya kammala a Shekara ta 1993.

Sheikh Ja’afar ya sami damar Kammala karatun digiri na biyu Masters a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da Take Khartoum a, Sudan daga nan ne kuma sheikh jafar ya fara aikin yada addinin musulunci da karantar da mutane musamman a masallacin sa na Almuntada dake unguwar Dorayi, wanda kuma anan ne wasu ‘yan bidiga suka harbe shi, a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 lokacin da ya ke limancin sallar Asuba wanda hakan  yayi sanadiyyar rasuwar sa.

Daga cikin karatuttukan da Sheikh Ja’afar  ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur’ani mai Girma, kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba’un Hadith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa’iz, Siffatus saltin nabiiy.

Da fatan Allah ya yi masa rahmah !

 

Continue Reading

Coronavirus

Corona Virus : An ki cin Biri an ci Dila

Published

on

Tun bayan bullar Murar mashako ta Corona Virus a karshen  Disambar shekarar data gabata a birnin Wuhan na kasar Sin wato China, zuwa yanzu haka annobar na kara fantsama fadin duniya inda yanzu haka sama da mutum dubu dari uku ne suka kamu da ita ,tare da mutuwar sama da dubu sha shida a fadin duniya.

Kasashe da dama, da hukumomi daban-daban,  attajirai , ‘yan wasa, dai -dai kun mutane da dubban likitoci da masana na ta bada gudunmowa ta fannoni daban -daban don ganin cewar an shawo kan wannan annoba da ta gagari Kundila.

Cutar wacce ake daukar ta ,ta hanyar yin mu’amala tsakanin al’umma kana mai saurin yaduwa ta cikin iskar da dan adam yake shaka tana bukatar taka tsan tsan da matakai daban -daban da masana kiwon lafiya suka bada shawarwari wajen rage yaduwar ta ,ciki har da killace kai da zama waje daya ba tare da mu’amala cikin dubbun nan jama’a ba.

Zuwa yanzu haka kama daga Saudi Arabia, Hadadiyar Daular Larabawa (UAE), Qatar, Amurka, Italiya  sun dau matakan rufe manyan gurare na Ibada, harkokin yau da kullum, makarantu, da guraren shakatawa da duk wani nau’i da zai hada cunkoson jama’a, tare da umartar al’ummar kasashen da kowa ya zauna a gida hukumomi zasu cigaba da biyan sa kudade da kuma samar musu da abubuwan bukatu na yau da kullum.

Tun bayan bullar cutar a kasar nan da wani dan kasar Italiya ya shigo da ita a jihar Lagos, cutar na kara yaduwa a fadin kasa wanda a yanzu haka ana da yawan mutum 46,  da suka kamu da cutar ciki har da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Malam Abba Kyari da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad sai dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, wato Muhammad Atiku.

Kamuwar wadannan mutane wanda kusan manyan turaku ne ko kuma mu kira su ‘Wuta da Batir ‘ ma’ana masu karfin iko ko fada aji da yadda zasu yi , ya sa shakku da tambayoyi a zukatan al’ummar kasar nan.Shin ina makomar kasar nan ,ma iya cewa kaikayi koma kan mashekiya ke nan ?

Wasu daga cikin tambayoyin da ke dar suwa a zukatan jama’a ke nan.In har gwamna guda mai rike da madafun iko da shugaban ma”aikatan fadar gwamnatin tarayya mai matukar iko da dan tsohon shugaban kasa mai matukar tasiri da wadata, zasu kamu , a ce a fadin kasa babu cikakkun kayan aikin da za’a kula dasu a Abuja, Bauchi da Adamawa, babu kuma damar fita zuwa kasashen ketare sakamakon killace kasashen  su da tsoron shigo musu da cutar ma iya cewa kaikayi ya koma kan mashekiya sakamakon shuwagabanni sun gaza wajen sauke nauyin dake wuyan su na yiwa al’umma hidima da samar musu da abinda yake a hakku kuma wajibi a matsayin su na ‘yan kasa.

Kama da ga sha’ani na lafiya ,Noma ,Ilimi da wutar lantarki ,tatalin arziki, kasuwanci, hanyoyi, tsaro na rayuka da dukiyoyin al’umma da makaman tansu zamu iya bada maki sifiri ga jagororin da suka rike a baya da wanda suke rike da kasar nan a yanzu sun gaza kwata -kwata ,illa iyaka kaurin suna wajen wasoson dukiyar talakawa da ajiye ta a asusun kasashen duniya da ba zai amfani al’ummar kasar nan ba.

A ya yinda wasu rahotannin sirri na bincike dangane da kadarorin da wasu ‘yan kasar nan suka mallaka a birnin Dubai, da ake zargin ta  hanyar yiwa tattalin arzin kasa zagon kasa da wasoso da dukiyar al’umma suka mallaka, wanda kudaden sun isa bunkasa kasar nan da wadatacciyar wutar lantarki ta dun -dun-din, tare da samar da ingantaccen harkokin kiwon lafiya  da cire kashi saba’in cikin dari na al’ummar kasar nan da ke fama da talauci , a gefe daya kayan agajin yaki da Cutar mai lakabin Covid 19, na  Attajirin da yafi kowa arziki dan kasar China Jack Ma, da ya taimaka wa kasashen duniya ciki har da kasar nan, sun sauka don cigaba da yakar cutar da takaita yaduwar ta.

Kowanne lamari yana zuwa da alfanu ko akasin sa, in har akwai yiwuwar killace al’umma da hanasu zirga -zirga ko fita neman na yau da kullum , shin wane tanadi hukumonin da suka kasa samar musu da kayan aikin inganta lafiyoyin su suka tanadar musu kasancewar su da ni sai mun fita kullum sannan mu samu  ‘yar tsabar da zamu kai baki ?Ina masu arzikin mu , mai suka tanadarwa al’umma a wannan hali na tsanani da ake ciki in har Jack Ma , zai taimaka tun daga kasar Sin ?Ma iya cewa alfanun cutar Corona, ya fara haskakawa shuwagabannin mu  son kan su da matsalolin su da rashin adalcin da suka dade suna yiwa al’ummar kasar nan.Fatan  mu a samu dalilai da zasu hana masu rike da  madafan iko samun mafaka, ajiye dukiya, neman lafiya ko wasu uzurin ba gaira ba dalili a kasashen Nahiyar Turai da Amurka ko kasashen da suka bunkasa ta dalilin jagoranci na gari.

Zuwa yanzu dai lamarin ya zama kaikayi koma kan mashekiya, kuma kukan kurciya da muke fatan jawabin yaje ga kunnen su , don kuwa lokaci ya yi da za  su karkato da tunanin  su wajen bunkasa kasar nan.

Continue Reading

Sharhi

‘Yar Atiku Abubakar ta kama sana’ar sayar da abinci

Published

on

Diyar tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ta baiwa al’ummar kasar nan mamaki,bayan bude gidan sai da abinci a birnin tarayya Abuja mai suna PIESTA RESTAURANT.

Walida wacce bata dade da kammala karatu ba a jami’ar Amurka dake birnin Yola na jihar Adamawa,  ta baiwa al’ummar kasar nan mamaki matuka kasancewar ana musu kallon shafaffu da mai kuma ‘ya yan wanda suke da ido, ko rike da madafun iko da ka iya samun babban aiki a ma’aikatun gwamnatin tarayya.Mahaifin Walida, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, da yake taya ta murnar bude wajen ya bayyana a shafin sa na Twitter kamar yadda kuke gani a kasa.

“ina alfahari da hazakarki ta kasuwanci. Kin kasance abin misali wajen koyar da matasa hanyoyin samar da ayyukan yi a kasa.”

Wannan dai na biyo bayan labarin da ya karade kasar nan na ‘yar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan wacce ta kama sana’ar daukar hoto jim kadan bayan ta kammala karatun ta na jami’a, a kasar Ingila.

Hanan Buhari ke nan lokacin daukar hotuna a Bauchi

A lokacin da dimbin matasan kasar nan ke neman gwamnati a dukkan matakai, data basu aiyyukan yi, sai gashi ‘ya yan masu hannu da shuni ko manyan mukarraban gwamnati da suka rike  madafun iko a baya ko a yanzu, na kokarin gina ‘ya ‘yan su bisa tafarkin rungumar sana’o’in dogaro da kai ta harkar kasuwanci a fanni daban–daban.

Sai dai a bangare daya al’ummar kasar nan na ganin cewar masu abu ne da abun su wato Kura da kallabin kitse, suke yin kidan su tare da yi rawar su kasancewar suna da karfin dukiyar da zasu kama ko fara sana’a kowacce iri da taimakon iyayen su wanda talakawa da dama ba su da jarin da zasu fara ko da karamar sana’a ce.

Karanta:

Hanan Buhari: Sana’a Maganin zaman banza

Ina fatan Allah ya bani sana’ar da tafi Kannywood -Mansur Makeup

Lokaci ya yi da gwamnatoci a dukkan matakai za su fito da sabbin tsare-tsare da zai taimaka ko saukakawa miliyoyin matsan kasar nan da basu da ayyukan yi, don su kama sana’oi don dogaro da kansu.

Suma daga bangaren su matasan ya kamata ace sunyi karatun ta nutsu, da tunanin samar wa da kansu mafita don yin abinda zasu dogara da kansu ba tare da zaman jiran gwamnati ba, duba da cewar  kasashe masu tasowa da wanda suka bunkasa,  sana’o’i da ayyukan dogaro da kai na kan gaba wajen samawa matasa ayyukan yi ba hukumomi ba.

 

Idan har diyar Atiku Walida za ta kama sana’ar sai da abinci, a gefe daya Hanan Buhari ta yi daukar hoto, wane dalili ne zai hana talakan kasar samar wa da kansa mafita ta hanyar sana’a?

 

Yanzu dai za a iya cewa lokaci ya yi da za mu farka daga jiran ko ta kwana kasancewar kasar nan tana da dumbin al’ummar da zata samar da kasuwa ga duk sana’ar da aka dauka don dogaro da kai.

 

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,535 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!