Connect with us

Coronavirus

Covid-19: Musulmai za su yi azumi kan Coronavirus

Published

on

Kungiyar limaman addinin musulunci na jihar Ogun sun shirya gudanar da addu’o’I da yin azumi kan samun waraka daga cutar COVID-19 na kwanaki uku.

Azumin wanda kungiyar tace za’a fara daga gobe Talata a cewar babban sakataren kungiyar Imam Tajudeen Adewunmi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar, kungiyar wacce aka fi sani da Rabidah z ata yi amfani da kwanaki masu alfarma na watan Sha’abban don yin Azumin kasancewar an samu barkewar cutar ta Corona a jihar Ogun.

Allah madaukakin sarki ne yake son nuna ikon sa kan yadda cutar ke ruruwa kuma da karfin sa ne komai za’a sami sauki cikin yarda Allah, a cewar kungiyar.

Akan haka ne kungiyar ta yi addu’ar Allah ya kawo kare kasar nan daga Annobar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,801 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!