Kiwon Lafiya
Covid-19: NMA ta bukaci membobinta da suka tsindima yajin aiki da su dawo aiki
Kungiyar likitoci ta kasa ta bukaci mambobin ta da suka tsunduma yajin aiki da su koma bakin aikin su don taimakawa wajen yaki da yaduwar cutar Corona a Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan da liktoci a babban birnin tarayya Abuja da Enugu da Gombe da Kaduna da Cross River suka tsunduma yajin aiki suna masu bukatar a biya musu bukatun su.
Shugaban kunhiyar na kasa Frabcis Faduyile ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a babban birnin tarayya Abuja, inda yace kungiyar ta kuma ce janye wannan yajin aikin ya zaman wajibi, la’akari da yadda cutar ke kara yaduwa a fadin duniya.
Kungiyar ta NMA ta ce duk da cewa tana bukatar gwamnati ta biya mata bukatun ta, amma bazata yi da watsi da halin da jama’a ka iya shiga ba sakamakon barazanar cutar corona don haka dole ne ta janye yajin aiki.
Sai dai kungiyar ta bukaci gwamnati da ta samar da kayayyakin kare kai da likitocin zasu yi amfani da su wajen kula da wadanda suka kamu da cutar ko da za’a samu barkewra ta a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login