Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Za a tsaurara dokar kulle a Jigawa

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa tace daga gobe Talata zata fara nuna halin babu sani ba sabo kan duk wanda ya yi wa dokar zaman gida karan tsaye a birnin Dutse.

Kwaminshinan ‘yan sandan jihar Jigawa Usman Sule Gamna ne ya yi wannan gargadi, sakamakon lura da ya ce hukumar su tayi ana yi wa dokar hawan kawara.

Kwaminshinan ya kara da cewa duk mai mota komai babur din da aka kama yana kara kaina babu wata hujja da doka ta amince da ita, to tabbas zasu yi ram dashi su kuma mika shi gaban kotu domin yi masa hukunci.

Labarai masu alaka:

Covid-19: An baiwa gwamnatin Jigawa tallafin kayan abinci kan Corona

Yadda dokar kulle ke gudana a Jigawa

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar jigawa SP Abdu Jinjiri ya yiwa Freedom Radio karin bayani inda yace, hatta masu shaguna dokar ta shafe su matukar dai ba hukuma ce ta basu dama ba, to za su fuskanci fushin kuliya manta sabo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!