Connect with us

Coronavirus

Covid-19: An baiwa gwamnatin Jigawa tallafin kayan abinci kan Corona

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa tace ta karbi tallafin kayan abinci tirela 93 daga gamayyar kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa, domin rabawa talakawa mabukata yayin dokar zaman gida ta sanadin corona.

Kwaminshinan lafiya kuma Shugaban kwamatin karta kwana a jihar Jigawa Dakta Abba Umar ne ya shaidawa wannan shiri haka da yammacin litinin din nan.

Kwaminshinan yace tuni suka fara aikin tan-tance wadanda ke sahun gaba ta fuskar bukata daga kananan hukumomin jihar, wanda a karon farko za’a fara bada tallafin da masu bukata ta musamman, kafin daga bisa ni a buda abin zuwa duk wani mai bukata.

Dakta Abba yace dama dai tuni sukayi rabon masara ga al’umma da kuma shinkafa da gero ga almajirai, a kananan hukumomin da dokar kulle ta shafa.

Labarai masu alaka:

Mutane 55 sun warke daga Corona a Jigawa

Yadda dokar kulle ke gudana a Jigawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,703 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!