Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Tambuwal ya sanya dokar takaita zirga-zirga a Sokoto

Published

on

Gwamnatin jihar Sokoto ta sanya dokar takaita zirga-zirga daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe.

Gwamnan jihar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana hakan cikin wani jawabi da ya yiwa al’ummar jihar a daren Lahadi.

Gwamna Tambuwal ya ce dokar zata fara aiki ne daga yau Litinin.

Har ila yau, Aminu Tambuwal ya roki al’ummar jihar Sokoto kan su mayar da hankali wajen bin dokokin da masana kiwon lafiya suka sanya wajen yaki da cutar ta Corona.

Ku kalli jawabin gwamna Aminu Waziri Tambuwal

A alkaluman ranar Lahadi da gwamnatin jihar Sokoton ta fitar, ta ce jihar tana da mutane 66 da suka kamu da cutar Covid-19.

Mutum 8 daga ciki sun warke sarai, kuma an sallamesu, sai mutum 1 da ya rigamu gidan gaskiya sanadiyyar cutar a jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!