Connect with us

Coronavirus

Mutum na 2 mai dauke da Corona ya rasu a Jigawa

Published

on

Da yammacin ranar lahadin nanne hukumomi a jihar Jigawa suka tabbatar da mutuwar mutum na biyu mai dauke da cutar Coronavirus.

Mai rasuwar dai wata matace daga karamar hukumar Miga, da aka gano tana dauke da cutar a baya-bayan nan, lokacin da yan uwanta suka kawota asibitin Jahun wadda daga bisani aka turasu asibitin kwararru na Rashid Shokoni dake Dutse, a nan kuma aka gano tana dauke da cutar.

Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito cewa, a farkon satin da ya gabata ne mutum na farko ya rasu sakamakon cutar ta Coronavirus, wadda shikuma yana daga cikin mutum biyu da aka samu dauke da cutar a karamar hukumar Dutse.

Mutane tara ne ke dauke da cutar a Jigawa biyu sun mutu, sauran bakwai kuma suna cikin hayyacinsu da kuma samun kulawar likitoci, a cibiyar killace masu dauke da cutar dake Dutse a cewar hukumomin lafiya a jihar Jigawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,693 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!