Connect with us

Labarai

COVID 19 : Za a hukunta wasu gwamnoni da take doka a filin jirgi

Published

on

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya yi barazanar gudanar da bincike kan yadda ake zargin wasu manyan kosohin gwamnati da suka take dokokin da aka shinfida a filin jiragen saman kasar nan a ya yin da aka sanya dokar kulle a kasar nan.

Hadi Sirika ya ce duk wanda aka kama yana da laifi toh babu shakka za’a garkame shi a gidan gyarin hali na watanni biyu

Ministan sufurin jiragen sama ya bayyana hakan a kwamitin shugaban kasa na dakile cutar Corona.

Ana dai zargin wasu manyan kososhin gwamnati uku da take dokar da aka sanya a filin jirgin saman kasar nan

Daga cikin akwai gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri da tsohon gwamna jihar Zamfara Abdul’aziz Yari da kuma wani mawallafin jarida.

Da yake maida martini kan korafe-korafen da ake yi kan wadannan masu fada a ji, Hadi Sarika, ya ce za’a hukunta duk wanda ya aikata hakan.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!