Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Zamu magance yawaitar cakuduwar jama’a-HISBAH

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce baza ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da bayar da gudunmawa ta bangarori da dama yayin da jihar ke rufe.

Babban kwamandan hukumar Hisbah Ustaz Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan, yayin zantawa da Wakilin Freedom Radio Umar Idris Shuaibu ta kafar sada zumunta ta WhatsApp.

Ustaz Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya ce hukumar ta maida hankali wajen ganin an dakile yawaitar dabdalar almajirai a fadin jihar Kano, don tabbatar da umarnin Gwamnatin Kano, a wani bangare na shawo kan annobar dake addabar al’umma a yanzu ta Corona da aka fi sani da COVID-19.

Kwamandan hukumar ta Hisbah ya kara da cewa, haka zalika na ci gaba da karbar koke-koken al’umma wanda suke bukatar agajin gaggawa anan birnin jiha, da kuma ofisoshinta dake kananan hukumomin Kano 44 don tabbatar da zaman lafiya da walwalar mutanen Kano baki daya.

Ustaz Harun Muhammad Sani Ibn Sina a yayin tattaunawar da yayi da Umar Idris Shuaibu, ya kuma bukaci iyaye wajen kula da kai-kawon ‘ya’yan su, kasancewar kananan yara na amfani da wannan dama ta zaman gida da ake ci gaba yi tare da wasanni musamman na kwallon kafa akan hanyoyi.

Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina ya kuma ja hankalin al’umma wajen ci gaba da yin biyayya ga dokar da Gwamnati ta sanya, duba da cewa an sanya ta ne don tabbatar da cewa cutar Corona bata ci gaba da yaduwa cikin sauri ba, da kuma daukar matakan da suka kamata daga bangaren Jami’an lafiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!