Connect with us

Labarai

Ba shiga ba fita a Gombe daga gobe Alhamis

Published

on

Gwamnatin jihar Gombe ta sanya dokar zaman gida da takaita cakuduwar jama’a daga karfe 6 na yammacin gobe zuwa karfe 7 na safe domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Gwamnan jihar Muhammadu Inuwa ne ya bayyana hakan ta cikin jawabin da ya gabatar a yammacin yau, inda ya ce gwamnati ta rufe dukkanin kasuwannin jihar da sauran tarukan jama’a na bukukuwa ko al’ada ko na ibada.

Wakilin mu Usman Abubakar Usmaniyya ya rawaito mana cewa gwamnan jihar ta Gombe ya dakatar da dukkan wata zirga-zirga daga wannan karamar hukumar zuwa wata karamar hukuma ba.

Sannan gwamnan ya ce dokar ba ta shafi masu ayyuka na musamman ba.

A kididdigar baya-bayan nan da cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta fitar ta ce izuwa yanzu mutane biyar suka kamu da cutar a jihar Gombe

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!