Connect with us

Coronavirus

Coronavirus ta bulla a Sokoto

Published

on

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce an samu bullar cutar Covid-19 a jihar Sokoto.

Cikin sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce an samu mutum guda dake dauke da kwayar cutar Covid-19 a jihar Sokoto.
Wakilin mu dake Sokoto Umar Ahmad Baffa ya shaida mana cewa tuni gwamnan jihar ta Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bada sanarwar samun mai dauke da cutar a jihar.

A sanarwar NCDC ta ce a yau Litinin an samu karin mutane 38 da suka kamu da cutar a sassan Najeriya.

Kididdigar NCDC ta daren Litinin dinnan ta ce yanzu haka Najeriya tana da mutane 665 da suka kamu da cutar, inda 188 daga ciki suka warke sarai, guda 22 kuma suka mutu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!