Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Cristiano Ronaldo ya zura kwallo uku a ragar Tottenham

Published

on

Dan wasan gaba na Manchester United da kasar Portugal Cristiano Ronaldo, ya zura kwallaye uku a wasan da tawagarsa tayi nasara da ci 3-2 a hannun Tottenham.

Filin wasa na Old Trafford dai shi ne ya karbi bakuncin wasan da ya gudana a ranar Asabar 12 ga Maris din 2022.

A minti na 12 Cristiano Ronaldo ya fara kwallon farko, kafin daga bisani ya kara kwallo ta biyu a minti na 38 da 81.

Daga bangaren Tottenham kuwa dan wasa Kane ya zura kwallo a minti na 35 a bugun daga kai sai mai tsaran gida, kafin kuma kyaftin din Manchester United Maguire ya zura kwallo a raga wato Own goal a turance.

Zuwa yanzu Cristiano Ronaldo ya sanya ya zama dan wasa na farko da ya fi kowa zura kwallo har sau uku da jumulla sau 59 a wakiltar kungiyoyi da kasarshi ta Portugal.

Haka zalika Manchester United ta koma maki na hudu da maki 50 a wasanni 29 da ta fafata a kasar wasannin shekarar 2021/2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!