Manyan Labarai
Cryptocurrency: Buhari zai ƙaddamar da tsarin kuɗi na e-Naira
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da tsarin gwajin kudin intanet a ranar Litinin.
Babban Bankin ƙasa CBN ne ya bayyana hakan a jawabin da daraktan yaɗa labarai na bankin Osita Nwanisobi ya yi a ranar Asabar.
A kwanakin baya ne dai babban bankin ƙasa CBN ya sanar da cewa zai ƙaddamar da tsarin kuɗin intanet da aka yiwa laƙabi da e-Naira a ranar 1 ga watan Oktoba.
Sai dai babban bankin ya ɗage ranar fara amfani da kuɗin intanet ɗin saboda bikin ranar samun yancin kai da aka gudanar a ranar.
Bankin na CBN ya ce, an fito da tsarin ne domin bayar da damar hada-hada ga sauran mutanen da ba sa samun damar shiga wasu hada-hadar kuɗaɗe.
Ya kuma bayyana cewa sabuwar kwandalar dijital ta e-Naira da za a fara amfani da ita, wani kudin hada-hada ne da za a rika amfani da shi baya ga Naira, kamar yadda dokar ƙasa ta amince da shi.
Kazalika bankin ya ce, za a fito da tsarin ne domin maye gurbin kuɗin Internet na “cryptocurrency” a ƙasar nan, wanda bankin CBN ya haramta amfani da su tun a watan Fabrairu saboda rashin gamsuwa da yadda tsarin sa yake.
You must be logged in to post a comment Login