Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi: CBN ya ƙara wa’adin daina amfani da tsoffin ƙudi

Published

on

Babban bankin ƙasa CBN ya tsawaita wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi.

Gwamnan CBN Godwin Emiefele ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai da safiyar Lahadin nan.

A cewar Emiefele ya ce ya samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karin wa’adin.

Yanzu haka dai babban bankin ƙasa CBN ya sanar da tsawaita wa’adin kwanaki 10 na daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira a fadin Najeriya.

A yanzu dai sabon wa’adin zai kasance 10 ga watan Fabrairu maimakon ranar 31 ga watan Janairu na daina amfani da ƙudin.

Ƙarin wa’adin y biyo bayan ganawar da shugaba Buhari ya yi da gwamnan babban ƙasa CBN Emefiele a garin Daura na jihar Katsina.

Ƴan Najeriya dai na da damar ci gaba canza takardar kudin Naira daga tsofaffi zuwa sababbi har zuwa wa’adin.

Idan za a iya tunawa tun a watan Oktoba CBN ya ɓullo da sabbin takardun kudi na naira 200, 500 da 1000 tare da bayar da wa’adin ranar 31 ga watan Janairu domin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin.

 

PremiumTime:

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!