Labarai
Cudanya da Hausawa ne ya sa na iya Hausa a Saudiyya- Dan Bangladesh
Wani dan kasar Bangladash mazaunin kasar Saudiyyya mai suna Muhyuddin yace bai taba zuwa kasar Hausa ba, amma zaman sa a birnin Makkah na kasar Saudiyya ne da cudanya da al’ummar Hausawa yasa ya iya harshen Hausa,
Muhiyyuddin ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da yayi da yan Najeriya mazauna kasar Saudiyya.
Akwai wata unguwa a brining Makkah da ake kira da dogon gida wadanda al’ummar Hausawa da dama ke zaune a yankin .
Muhiyyudin yace bai taba zuwa Najeriya ba ko jamhuriyar Nijar ,amma cudanya da Hausawa ne a dogon gida yasa ya iya harshen Hausa.
Mutumin dan kasar ta Bangladesh ya kara da cewa a hankali ya rika kokarin koyan harshen na Hausa.
Yace bait aba cin abincin Hausawa ba amma ya taba cin tsire .
Muhuyyiddin yace sanaarsa a kasar ta Saudiyya itace sayar da jallabiyya kuma nan gaba yana muradin ya zo Najeriya da niyyar ziyartar wasu jihohi.
Saurari cikakkiyar tattaunawar da akayi dashi:
Ayi sauraro lafiya.