Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abubuwan da ya kamata ku sani game da ranar harshen Hausa

Published

on

Ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ce ake gudanar da bikin ranar harshen Hausa ta duniya.

Yau shekaru shida kenan da wasu fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta a ƙasar nan suka ƙirƙiro ranar, wadda kuma suka keɓe domin bikin ranar a kowace shekara.

A duk sanda ranar ta zagayo hausawa masu amfani da shafukan sada zumunta na amfani da maudu’in #RanarHausa domin murnar bikin, tare da wallafa rubuce-rubuce cikin harshen Hausa.

Rubutukan da aka fi wallafawa sun haɗa da karin magana da salon zance a harshen Hausa, da kuma rubutukan ƙarfafa gwiwar jama’a kan su riƙa amfani da harshen Hausa.

Haka kuma ana gabatar da taruka domin tattauna batutuwan da suka shafi harshen na Hausa.

A shekarar 2019 an ƙiyasta mutane fiye da 400,000 ne suka gudanar da bikin ranar ta internet.

Albarkacin raya ranar a shekarar 2019, masana sun gabatar da maƙaloli a wani babban taron ɗaliban Hausa na duniya da aka gabatar a jami’ar Bayero, da ke nan Kano inda suka bayyana bunƙasar da harshen Hausa ke samu a duniya.

Sai dai kuma har yanzu masana na kukan cewar tasirin Turawan mulkin mallaka na ci gaba da kawo cikas wajen harkar koyo da koyarwa da harshen Hausa, lamarin da ke zama ƙalubale ga harshen.

Binciken masana a fannin harshe ya dora harshen Hausa a matsayin harshe na 11 da aka fi amfani da shi a duniya.

Harshen da ke a matsayin na farko a duniyar shi ne harshen Mandarin sai Inglishi da ke biye masa baya yayin da harshen Hindu na ƙasar India ya zamo na uku.

Harshen Hausa na ci gaba da burunƙasa yana lamushe harsuna da dama wadanda galibinsu sun fuskanci yankan kunkurun Bala daga harshen na Hausa.

To amma rashin mayar da kai ga Hausawa wajen koya wa masu tasowa kishin harshen na barazanar yi wa harshen na Hausa tashin tantabarun Hudu.

Dan haka ne ma masana ke kira da a hada kai domin magance tarnaƙin da harshen ke fuskanta.

Sai dai a yayin Maƙala da ya gabatar yayin wannan gagarumin taro, farfesa Aliyu Bunza na jami’ar Usmanu Danfodio dake Sokoto ya bayyana cewar har yanzu da sauran rina a kaba, domin rashin amfani da harshen Hausa wajen koyar da ɗalibai a makarantu ya zama wani babban al’amari da ke zamar wa Hausawa tukin tuwon tulu.

Sai dai cibiyar nazarin harshen Hausa da ke jami’ar Bayero ta ce ta fara kamo bakin zaren wannan matsala, har ma Farfesa Aliyu Mu’azu ya ce tuni suka fara samar da litattafan kimiyya da aka wallafa da harshen Hausa.

Aminu Suleman Goro shi ne shugaban kwamitin ilimi na majalisar tarayyar Nigeria ya halarci wannan taro yana mai alƙawarin cewar za su duba yiwuwar shigar da litattafan cikin manhaja domin ganin an fitar da A’i daga Rogo.

Yayin bikin farar kaza balbela an ce ba gayya ba ce, domin wasu Sinawa masu magana da harshen Mandarin wanda aka ce shi ne ya fi kowane yawan mutane a duniya kuma suke koyon Hausa sun halarci taron cikin murna da farin ciki tare da bayyana dalilinsu na karɓar shahadar koyon harshen na Hausa.

Yayin wannan taro an nada Kwamared Nura Suleman a matsayin sarkin ɗaliban Najeriya.

Sai dai kuma babban abin da ke damun Hausawa shi ne matsalar rashin haɗin kai a tsakanin juna domin shi kansa wannan taro na raya ranar Hausa ta duniya, an yi farraƙu wajen gabatar da shi inda wasu masu taron suka gabatar da nasu taron daban a gidan dan Hausa da ke nan Kano.

A wannan shekarar duk da cewa ta zo cikin halin yaƙi da annobar Corona amma wasu ƙungiyoyi sun shirya gudanar da taron bikin ranar.

NSZ

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!