Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

A fara duba jinjirin watan Safar-Sarkin Musulmi

Published

on

Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin sabon watan Safar na bana a daga yau Lahadi 29 ga watan Satumba, wanda ya yi dai dai da 29 ga watan Muharram.

Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka raba wa manema jabarai a jihar Sokoto wadda shugaban kwamitin bada  shawarwari kan harkokin addinin musulunci Farfesa Sambo Junaidu ya fitar.

Sanarwar ta bukaci al’ummar musulmin da suka ga jinjirin watan da su sanar da hakimansu domin sanar da fadar ta sarkin musulmi.

Mai alfarma sarkin musulmin ya kuma bukaci al’ummar musulmin da su rika taimakawa ‘yan uwansu musulmi wajen gudanar da ayyukan ibadun su yadda ya kamata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!