Labaran Wasanni
Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni
Hukumomin gudanar da kwallon kafa a kasar Andalus, wato Spain sun tabbatar da cewar za’a fafata wasannin manyan kungiyoyin rukuni na daya da na biyu, na tsawon mako biyu ba tare da ‘yan kallo ba sakamakon barazanar yaduwar cutar Corona virus.
Wasan Eibar da Real Sociedad, za ayi shi ba tare da ‘yan kallo sun shiga ba haka kuma rahotanni sun tabbatar da cewar hukuncin dakatar da ‘yan kallon zai fara tun daga yau Talata.
Hukumar ta La liga, ta ce ta dau matakin ne biyo bayan shawarar da Ma’aikatar lafiya ta kasar ta bayar, a ta bakin shugaban sashen lafiya na yankin Catalonia, Joan Guix.
Labarai masu alaka.
Yadda wasannin zakarun nahiyar Turai ke gudana
Dalilan dakatar da wasanni a birnin Tokyo
Zuwa yanzu haka wasu manayan wasanni da suka hada da, wasan Barcelona da Napoli a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, da wasan Sevilla da As Roma sai wasan Getafe da Inter Milan a gasar cin kofin Kalubale, na nahiyar Turai wato Europa league, da wasan Paris Saint German da Borussia Dortmund, a gasar zakaru nahiyar turai, champions league duk za’a fafata su ba ‘yan kallo.
Sai wasan Manchester United da LASK Linz ta kasar Austria, da shima hakan ta shafe shi ba tare da ‘yan kallo.
You must be logged in to post a comment Login