Labarai
Cutar Sankarau ta kashe yara 60 a Kebbi

Yayin da cutar Sankarau ke ci gaba da yaduwa cikin gaggawa a wasu daga cikin hohin Arewacin kasar nan, rahotonni sun tabbatar da mutuwar yara 60 a kananan hukumomin Gwandu da Jega da kuma Aliero na jihar Kebbi.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar bayar da agaji a fannin lafiya ta Medecins Sans Frontieres MSF da aka fi sani da Doctors Without Borders ke ci gaba da yin gargadin daukar matakan kare kai daga kamuwa da cutar.
Haka kuma kungiyar, ta bukaci da a dauki matakin gaggawa wajen dakile yaduwar cutar wadda zuwa yanzu fiye da mutane 500 suka kamu da ita a yankunan Gwandu da Jega da kuma Aliero.
A cewar wani Likita da ke aiki da kungiyar Dakta Bukar Galtimari, akwai bukatar a rika yin gaggawar kai wadanda suka kamu da cutar asibiti domin ceton lafiyarsu kasancewarta cuta mai matukar hatsari.
You must be logged in to post a comment Login