Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Cutar yellow fever ta kashe mutane 76 a Najeriya – NCDC

Published

on

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce akalla mutane 76 ne suka rasa rayukansu sanadiyar cutar shawara wato Yellow fever cikin kwanaki 11.

 

NCDC ta ce, cutar ta bazu a jihohi uku na arewacin kasar nan da suka hadar da Delta da Bauchi da kuma Enugu.

 

Ta cikin rahoton da cibiyar ta wallafa a shafinta na Twitter a daren jiya juma’a ta ce daga bullar cutar a ranar 1 ga watan da Nuwambar da muke ciki zuwa 14 a kalla mutane 74 ne suka rasu sanadiyyar cutar.

 

A cewar NCDC tuni ta baza jami’anta zuwa lunguna da sakuna na jihohin da aka samu bullar cutar da nufin dakileta, sai dai a yanzu haka mutane sha tara ne ka fama da cutar a jihohin.

 

 

NCDC ta kuma ce a jihar Delta mutane 74 ne suka kamu da cutar yayin da 35 suka rigamu gidan gaskiya sai jihar Enugu wanda mutane 70 suka harbu da cutar yayin da 33 suka mutu.

 

Ita kuwa jihar Bauchi da 78 suka kamu yayin da 8 suka rasa rayukansu.

 

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!